2 Timothy 3

1Amma ka san da wannan: a cikin kwanakin karshe za a yi lokuta masu matsananciyar wahala. 2Gama mutane za su zama masu son kansu, masu son kudi, masu Kumburi, da girman kai, masu sabo, marasa biyayya ga iyaye, marasa godiya, da kuma marasa tsarki. 3Za su kasance marasa dabi’a, wadanda basu son jituwa da kowa, masu tsegumi, marasa kamun kai, ‘yan tawaye, marasa kaunar nagarta. 4Za su zama masu zagon kasa, taurin kai, masu takama, da masu kaunar anishuwa fiye da kaunar Allah.

5Za su kasance da siffar ibada amma za su musunci ikonta. Ka juya daga wadannan mutanen. 6A cikinsu akwai wadanda suke shiga gidaje suna yaudarar mataye marasa hikima. Wadannan ne mataye wadanda suke cike da zunubi, kuma sun kauce hanya sabili da sha’awoyi dabam daban. 7Wadannan matayen suna ta koyo, amma ba za su taba kai wa ga sanin gaskiya ba.

8Kamar yadda Yannisu da Yambrisu suka yi jayayya da Musa. Haka nan wadannan malaman karya kuma suke yin tsayayya da gaskiya. Mutane ne lalatattu a zuciya, marasa sahihiyar bangaskiya. 9Amma ba za su yi nisa ba. Domin wautarsu za ta bayyana a fili ga kowa, kamar wadannan mutane.

10Amma kai, ka bi koyarwata, da dabi’ata, nufe nufena, da bangaskiyata, da jimriyata, da kaunata, da hakurina, 11da yawan kuncina, da wahalolina, da duk abubuwan da suka faru da ni a Antakiya, da Ikoniya da kuma Listra. Na jure a cikin kuncina. Amma a cikinsu dukka, Ubangiji ya cece ni. 12Duk wadanda su ke so su yi rayuwa ta ibada a cikin Almasihu Yesu za su sha tsanani. 13Miyagun mutane da masu hila za su yi ta kara lalacewa. Za su badda wasu. Su da kansu ma sun bijire.

14Amma kai, ka ci gaba da abubuwan da ka koya kuma ka gaskata da zuciya daya. Ka san daga wurin wanda ka koya. 15Ka san da cewa, tun kana dan karamin yaro ka san wadannan littattafai masu tsarki. Wadannan suna iya mai da kai mai hikima domin ceto ta wurin bangaskiya a cikin Almasihu Yesu.

16Dukkan Nassi hurarre ne daga Allah. Yana da amfani domin koyarwa, domin tsautawa, domin gyara, kuma domin horarwa cikin adalci. Wannan domin mutumin Allah ya zama cikakke ne, shiryayye domin dukkan ayyukan nagarta.

17

Copyright information for HauULB